A wani rahoto daya saba fitarwa kowace shekara, shafin Global Fire Power mai nazari kan harkar tsaro da kwarewar sojoji a Duniya ya zayyano kasashen Amurka, Rasha da China daya bayan daya a matsayin wadanda suka fi kwarewa a harkar soji da kayan aiki Duniya.
Shafin ya kuma Ambato kasashen Mali, Mozanbique da Somaliya a mastayin kutal a wannan fani.
Kazalika a nahiyar Afirka rahoto ya zayyano kasashen Masar, Aljeriya, Afirka ta Kudu da Najeriya a mastayin na gaba wajen kayan aiki da kuma kwarewa a sha’anin tsaro da soji.
A wannan rahoto kuma shafin na Global Fire Power ya rawaito Kasar Nijar a matsayi na 10, yayinda kasar Cadi ke matsayi na 12.